<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ga mutum mai ƙazamin Ruhu
 Ya gamu da Yesu dai
 Kullum kuwa ko dare da rana
 Yana kururuwa dai.
 Ya tsatsage jikinsa kuwa
 Can kabari da duwatsu.

[V2]
 2) Ba wanda na da iko shi damre
 Mai ƙazamin Ruhun nan
 Sau da yawa ya tsutsunke
 Har sarƙoƙi ya karye su.

[V3]
 3) Sai ya iske Yesu na zuwa
 Daga nesa ya iske shi
 Ya sheƙo a guje domin
 Ya yi masa sujada fa.

[V4]
 4) Ya ce &quot;ina ruwana da kai,
 Yesu kai Ɗan Allah ne ?&quot;
 Ya ce &quot;Ka fito daga cikin
 Mai ƙazamin Ruhun nan.&quot;

[V5]
 5) Ҡazamin ruhohin nan
 Sun shiga cikin gursunnai
 Su sun faɗi cikin teku
 Sun nutse dai, sun shaƙe kuwa.

[V6]
 6) Ta wurin ikon Maɗaukaki
 Yesu Ɗan Allah kaɗai
 Mai ƙazamin ruhun ya zama
 Mai hankali, mai shaida kuwa.

[V7]
 7) Sai mu bi Yesu don ya iya
 Cece mu daga Shaiɗan.
 Mu gaskanta shi Ɗan Allah ne
 Mai Cetonmu, Mai Kamnarmu.</lyrics>
<title>Ga Mutum Mai Ƙazamin Ruhu LW413</title>
<hymn_number>413</hymn_number>
</song>